1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin shugabanci ya mamaye NDC a Ghana

January 27, 2023

Ana ci gaba da yin martani mabanbanta dangane da matakin jagororin babbar jam’iyyar adawar Ghana na tsige shugaban jam’iyyar da mataimakinsa a majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/4Mo9w
Ghana Parlament
Hoto: Isaac Kaledzi/DW

A yayin da sabbin jagororin suka fara yin bayanai har da ganawa da 'yan jarida, jiga-jigan jam'iyyar ta NDC har da tsohon jogorarta Cletus Avoka, ya ce sauyin bai wanzu ba musamman kasancewar majalisa na cikin hutu. Kuma wajibi ne sai da sahalewar kakakin majalisar bayan gabatar masa da aniyar jam'iyya, a tantance kuma a rattaba hannu kafin a iya yin wani sauyi.

Bayan sanar da canjin dai an yi cece-ku-ce har da tada husuma a mazabun jagororin da aka tsige inda daga bisani tarzoma ta kwanta. Amma duk da haka magoya bayan jami'ayya tun daga kasa sun nuna rashin jin dadi.

Matakin da ya zo a daidai lokacin da kuri'un jin ra'ayi ke nunin jama'ar Ghana na zumudin ganin sauyin gwamnati mai ci wadda ta yi silar tankewar kumci da matsin tattalin arziki da ake fama kuma yanzu watakila ita NDCn ta samu rarrabuwar kawuna sakamakon wannan.

Sai dai sabon shugaban jami'iyyar ya ce canji kan an yi kuma babu ja da baya duk kuwa da guna-gunin cewar yin hakan tamkar yi wa kai hasabi ne tare da hawan siratsin halaka a zabukan shekarar 2024 mai karatowa.