1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Larabawa sun soki matakin Turkiyya a Siriya

Mahamud Yaya Azare
October 10, 2019

Kasashen Larabawa na mayar da martani bisa matakin dakarun Turkiyya na ci gaba da yin lugudan wuta kan yankunan arewa maso gabashin Siriya domin fatattakar mayakan sa kan Kurdawa.

https://p.dw.com/p/3R4t3
Syrien Ras al Ayn Militäroffensive der Türkei in Nordsyrien
Hoto: picture-alliance/dpa/AP

A daidai lokacin da dakarun Turkiyya ke ci gaba da yin lugudan wuta kan yankunan Arewa maso gabashin Siriya,don fatattakar mayakan sa kan Kurdawa, kasashen Larabawa na ci gaba da yin suka da kakkausar murya ga farmakin da  suka siffantashi  da mummunan cin zalun da ya keta hurumi da diyaucin kasar ta Siriya.

Türkei Stadt Akcakale Militaerfahrzeuge vor Krankenhaus
Hoto: DHA

Kasar Masar wacce take kulle da Turkiyya kan bai wa 'yan kungiyar 'Yan uwa Musulmi da take dauka yan ta'adda mafaka da ba su damar kafa kafofin watsa labaran da ke caccakarta da tonon silili, ta  nemi kungiyar kasashen Larabawa da ta shirya taron gaggawa kan batun a ranar Asabar, don daukar matakin bai daya na Larabawa dangane da abin da ta kira hare-haren share fagen dawo da mulkin mallaka na Turkawa ga kasashen Larabawa.

Ita kuwa Saudiyya ta shiga takun saka da kasar ta Turkiyya, bayan da Turkiyya ta saka a gaba kan neman sanin hakikanin wadanda ke da alhakin kasha dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ta Saudiya SPA ya ruwaito, hankalin Masarautar ya yi matukar tashi da hare-haren cin zalin Turkiyya kan Siriya, hare-haren da ke iya wargaza dogon yunkurin da ake ta yi na murkushe 'yan ta'adda a yankin.

Shi ma Shugaban Barham Saleh na kasar Iraki ya rubuta a shafinsa na Twitter kan cewa hare-haren na Turkiyya babu abin da za su tsinana ban da kara karfafawa 'yan ta'adda karfi a yankin da ke ci gaba da tafarfasa.

Syrien Konflikt Grenze Türkei | Türkischer Panzer
Hoto: picture-alliance/Zuma Press/Turkish Defense Ministry

Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, kira suka yi ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki alhakin da ya rataya a wuyanta don hana kisan kare dangin da suka ce Turkiyya ta saba yi, ga alumomin Kurdawa.

Tuni dai shugaban kungiyar kasashen Larabawa, Ahmed Geit ya aminta da yin taron kasashen na Larabawa a ranar Asabar kamar yadda Masar ta nema, yana mai cewa, dole ne a tashi haikan kan hana aukuwar sabon bala'i a cikin kasashen na Larabawa.

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Althani da ke zama babban abokin dasawa na kasar ta Turkiyya, kamar yadda tashar tabalijin ta kasar ta ruwaito ya buga waya ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya suka tattauna halin da ake ciki a yankin.