Yaya rikicin Gabas ta Tsakiya zai kaya?
October 2, 2024Tuni manyan kasashen kamar Birtaniya firaministan kasar Keir Starmer ya tabbatar wa takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu cikakken goyon bayansa, tare da yin tir da matakin Iran na kaddamar da hare-haren rokokin. Firaminista Starmer ya ce babu wanda zai amince da matakin Iran na harba makamai masu linzami kusan 200, kuma abin da mahukuntan Iran suke bukatar gani shi ne kassara fararen hula na Isra'ila. Shi ma Firaminista Anthony Albanese na kasar Australiya, na cikin shugabannin kasashen duniya da suka tir da matakin na Iran. cikin sanarwar da ministan harkokin wajen Isra'ilan Israel Katz ya fitar, Isra'ila ta nuna mamakin yadda sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gaza yin tir da wannan hare-hare na Iran tare da haramta masa sake shiga kasar.
Gwamnatin Isra'ila ta yi barazanar cewa za ta dauki fansa game da makaman roka da Iran ta harba zuwa kasar. A hannu guda kuma Iran din ta ce muddun Isra'ila ta yi yunkurin kai mata hari, za ta lalata kayayyakin more rayuwan Tel Avivi din. Wannan rikici na yankin Gabas ta Tsakiya da tsoron yuwuwar barkewar yaki a yankin, ya janyo tashin farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya. Muddun wannan rikici na yankin Gabas ta Tsakiya da ake fargabar yiwuwar rincabewarsa ya gawurta farashin danyen man fetur zai ci gaba da tashin gwauron zabi, saboda tasirin kasashen wajen fitar da man fetur zuwa kasashen duniya.