1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan ikirarin Jonathan game da Pilato

July 18, 2012

Ana ci gaba da baiyana mamakin jawabin Goodluck Jonathan inda ya wanke Boko Haram daga zargin hare-hare a jihar Pilato

https://p.dw.com/p/15ZxN
Hoto: picture-alliance/dpa

Yayinda a karo na farko gwamnatin Tarayyar Najeriya ta wanke kungiyar Boko Haram daga munanan hare-hare da ake kaiwa a wasu sassan Tarayyar Najeriya wanda yayi sanadiyyar rayuka da dama, masharhanta da kungiyoyin fararen hula gami da talakawa sun fara tofa albarkacin bakin su.

Duk da cewa kungiyar nan mai gwagwarmaya da makamai don tabbatar da bin tsarin shari'ar musuluncin a tarayyar Najeriya ta yi ikirarin kai hare-hare na baya-bayan nan a jihar Filato Shugaba Goodluck Jonathan ya musanta cewa ba kungiyar ce ke da alhakin kai munanan hare-haren ba. Wannan dai shine karo na farko da gwamnatin kasar ta fito ta wanke kungiyar karkashin jagorancin Imam Abu Muhammad Abubakar Ibn Muhammad Shekau daga zargin kai hare-haren da ake kaiwa a sassan kasar.

Wannan ya sa kungiyoyin fararen hula da masharhanta gami da talakawa yin Allah wadai da wannan furuci na shugaban inda suke zargin cewa ana son shafawa wasu kabilu ko ‘yan adawa kashin kaji ne kawai ganin ba'a kai ga fidda bayanai kan binciken da ake kan gudanarwa dangane da wannan hare-hare ba. Ado Muhammad Jekadafari Gombe wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya.

Nigeria Normaden Fulani Hütten bei Abuja
Sojoji sun rushe matsugunan Fulani a PilatoHoto: dapd

Talakawan kasar zargi shugaban suka yi da rashin iya magana, gami da yin shishigi a lamuran bincike don gani musabbabin irin wannan tashe-tashen hankula, wanda hakan a ganinsu kasawa ne a bangaren shugabancin kasar. Kungiyoyin kare hakkin bani Adama kuma kalubalantar shugaban suka yi ya bayyana wadanda suke kai hare-haren, tunda ya san wanda suka kai kamar yadda Yusuf Haruna daya daga cikin masu yaki da cin zarafin bani Adama ya shaida min. Ko me yakamata ayi a irin wannan Yanayin dai Ado Musa yace:

Shugaba Jonathan ya kuma bayyana cewa nan kusa gwamnatinsa zata kawo karshen ayyukan kungiyar gwagwarmayar, wanda ke haifar da barazana ga tsaro da hadin kan kasar, abinda masharhanta suka bayyana da cewa kurari ne irin wanda gwamnatin ta saba amma babu abinda zata iya yi don matsalar tafi karfin ta .

In this Wednesday, Sept. 28, 2011 photo, police officers armed with AK-47 rifles stand guard at sandbagged bunkers along a major road in Maiduguri, Nigeria. The radical sect Boko Haram, which in August 2011 bombed the United Nations headquarters in Nigeria, is the gravest security threat to Africa's most populous nation and is gaining prominence. A security agency crackdown, which human rights activists say has left innocent civilians dead, could be winning the insurgency even more supporters. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Kalubale kan sojoji game da kiyaye tsaro a NajeriyaHoto: dapd