1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan shirin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Zainab Mohammed Abubakar GAT
January 29, 2020

Kasashen duniya na ci gaba da bayyana matsayinsu kan shirin Shugaba Donald Trump na Amirka na zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, a yayin da MDD ta jaddada matsayinta na sansanta Isra'ila da Palasdinawa.

https://p.dw.com/p/3WzWm
USA Israel Donald Trump und Ministerpräsident Benjamin Netanjahu
Hoto: picture-alliance/Consolidated News Photos/CNP/J. Lott

Majalisar Dinkin Duniya ta sake jaddada matsayinta kan kokarin sasanta rikicin yankin Palasdinu da Izra'ila, duk kuwa da matakin da Amurka ta dauka na nuna bangarenci. Tuni dai kasashen duniya suka fara mayar da martani kan shirin Shugaba Donald Trump na samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. 

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani dangane da shirin shugaban na Amurka kan abun da ya kira na sasanta rikicin Izra'ila da yankin na Palasdinu. Duk da cewar Shugaba Benjamin Netanyahu ya karbi shirin da hannu biyu, Palasdinawa sun yi watsi da shirin da suka ce, wani yunkuri ne na hana su kafa kasarsu ta kansu.

A hirarsa da manema labaru a birnin New York, kakakin babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Stephan Dujarric ya shaidar da cewar, babu gudu ba ja da baya dangane da manufofin da aka cimma a shekarun a baya a zauren majalisar kan matakan warware matsalar bangarorin biyu:

UN Sprecher Stephane Dujarric ARCHIV 2018
Stephane Dujarric kakakin babban magatakardan MDDHoto: picture-alliance/Photoshot/L. Muzi

"Abun da ke da akwai shi ne, Majalisar Dinkin Duniya ba za ta sauya matsayinta ba, za ta ci gaba da martaba duk wani kuduri na kwamitin sulhu da na zauren majalisar, walau a kan cimma yajejeniya a kan matsugunnai, ko kuma matsayin birnin Kudus, batun da shekara da shekaru ake kokarin cimma matsaya ta dindindin a kansa tsakanin bangarori biyun da abun ya shafa"

Faransa a nata bangaren ta yi maraba da sabon yunkurin shugaban Amurka Donald Trump na warware rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya, sai dai ta ce za ta yi nazarin abubuwan da shirin ya kunsa. Mahukuntan na Paris dai na ganin cewar hanya guda ta warware wannan rikici ita ce, samar da kasashe guda biyu masu makwabtaka da juna, idan har za a bi ka'idojin kasa da kasa na cimma zaman lafiya na dindindin a yankin na Gabas ta Tsakiya. 

A sharhinta na wannan Larabar, jaridar Frankfurter Rundschau da ke fitowa kowace rana a nan Jamus, ta ce shirin zaman lafiyan da aka gabatar ya zo a kan gaba, kasancewar mutane biyun da suka gabatar da shi na cikin wadi na tsaka mai wuya a fagen siyasar kasashensu. A cewar sakataren yada labaru na shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov, suna nazarin shirin, a daidai lokacin da Shugaba Vladimir Putin ke shirin ganawa da takwaransa na Izra'ila a gobe Alhamis:

Russland Moskau Putins Präsidenten Sprecher  Dmitry Peskov
Dmitry Peskov sakataren yada labarai na Shugaba Putin.Hoto: picture-alliance/dpa/TASS/M. Metzel

"Ya zuwa yanzu za mu iya cewar, Izra'ila ta karbi shirin hannun biyu-biyu, kana ya samu goyon bayan wasu kasashe, a yayin da wadanda shirin ya shafa kai tsaye watau Palasdinu, suka yi watsi da shi. A halin yanzu wannan ne matsayin da ake kai. Rasha za ta ci gaba da taka tata rawa a matsayin daya daga cikin bangarori hudu masu kokarin warware matsalar yankin Gabas ta Tsakiya. Idan da hali, Rasha za ta ci gaba da kokarinta na ganin cewar, an cimma manufa da aka sanya a gaba ta samar da zaman lafiya a wannan yanki".

Tuni dai Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya yi Allah wadai da shirin na Trump, da jaddada cewar ba zai samu amincewa ba. Erdogan ya ce Birnin Kudus wuri ne mai tsarki ga al'ummar Musulmi. Matakin bai wa Izra'ila yankin ba abu ne mai yiwuwa ba. Wannan shiri ya take 'yancin al'ummar Palasdinu, tare da halatta yankunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna. A cewar shugaban na Turkiyya dai, shirin ya kunshi bai wa  Palastinawa kasarsu ta kansu amma da sharudda masu tsauri, da suka kunshi bukatar rusa rundunar sojinsu nan gaba. 

Dangantakar Turkiyya da Izra'Äila dai ya yi tsami saboda, yadda Ankara ke gaba gaba wajen kokarin ceto wa Palastinawa 'yancinsu.