1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon malamin makaranta ya lashe zaben Tunisiya

Mahmud Yaya Azare MNA
October 14, 2019

Al'ummar Tunisiya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan sakamakon farko na zaben shugaban kasar da ke nuni da cewa, dan takara mai ra'ayin mazan jiya, Farfesa Kais Saied shi ya lashe zaben.

https://p.dw.com/p/3RGGG
Kaïs Saïed hat die Wahl in Tunesien gewonnen
Hoto: AFP/F. Belaid

  Da kashi sama da 70 cikin 100 ne dai Kais Saied ya lashe zaben shugaban kasar da ke zama irinsa na uku a kasar tun bayan juyin juya halin da ya yi awon gaba da mulkin marigayi shugaba Zainul Abidine bin Ali. Kais Saied ya siffanta nasarar tasa da bude sabon shafi a tarihin kasar Tunisiya.

   "A yau za mu fara kokarin gina kasar Tunisiya da karfin dantsenmu. Kasar Tunisiya za ta bawa marada kunya. Za ta tsaya da kafafuwanta. Da wannan zaben nawa da kuka yi, kun sake nuna wa duniya cewa, ba abin da zai gagareku. Kuma idan kuka yi nufin aikata abu, da yardar Allah sai kun yi."

Shi ma abokin karawarsa, Nabeel Karawei, wanda ya aminta da shan kaye ya danganta hakan da karancin lokacin yin kamfen da ya yi sakamakon daureshi da aka yi.

"Abin da ya faru a yayin wannan zaben abin alfahari ne ga kasar Tunisaya. Na yi amannar ba ku yi zaben tumun dare ba. Kamar yadda na yi amannar cewa, da na samu isasshen lokaci irin na abokin takarata wurin bayyana muku kyawawan manufofi na, da kuri'ar da za ku ba ni sai ta dara haka."

Magoya bayan Kais Saied sun yi ta murnar nasarar lashe zaben da ya yi
Magoya bayan Kais Saied sun yi ta murnar nasarar lashe zaben da ya yiHoto: Reuters/A. Ben Aziza

Da dama daga cikin wadanda suke shagulgulan nasarar ta Kais Saied suna daukar wannan nasarar tasa, tamkar ita ce nasarar juyin juya halinsu.

"A yau mun yi wani juyin juya hali ta akwatunan zabe, bayan wanda muka yi ta zanga-zanga kan tituna. Mun zabi wanda muke kyautata zaton zai aiwatar da taken da muke ta rerawa, wato kawo sauyin da za a gani a kasa da gyara-gyare."

Zaben shugaban kasar dai ya yi matukar ba zata ga masu sa ido, yadda illahirin 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasa suka sha kaye tun a zagayen farko na zaben. Shi kansa Nabeel Karawei, da ake zargin ya yi amfani da kudi da raba kayakin masarufi, irin wannan tsohon salon da 'yan siyasar kasashe masu tasowa suka yi kaurin suna wajen binsa, bai haifar masa da wani abin kirki ba.

Wasu daga cikin 'yan Tunisiya kira suke ga 'yan uwansu da ke sauran kasashen Larabawa da su yi koyi da su wajen samar da sauyi a kasashensu cikin lumana.