1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mohammed-Karikaturen

Usman ShehuSeptember 20, 2012

An fara maida martani kan zanen ɓatanci da wata jarida a ƙasar Faransa ta wallafa kan addinin Islama

https://p.dw.com/p/16Bxa
Publishing director of the satyric weekly Charlie Hebdo, Charb, displays the front page of the newspaper as he poses for photographers in Paris, Wednesday, Sept. 19, 2012. Police took up positions outside the Paris offices of the satirical French weekly that published crude caricatures of the Prophet Muhammad on Wednesday that ridicule the film and the furor surrounding it. The provocative weekly, Charlie Hebdo, was firebombed last year after it released a special edition that portrayed the Prophet Muhammad as a "guest editor" and took aim at radical Islam. (Foto:MIchel Euler/AP/dapd)
Stéphane Charbonnier, babban editan jaridar Charlie HebdoHoto: dapd

A ƙasar Faransa jiyane wata mujalla mai yin shaguɓe ta sake wallafa zanen ɓantanci ga Manzon Allah Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata agare shi. Duk da cewa Firayim ministan ƙasar ta Faransa da ma ministan harkokin waje duk sun nuna damuwa bisa wannan matakin da zai ɓata ran ma biya addinin Islama.

Jaridar da aka sani da Charlie Hebdo a shafinta na wannan mako ta nuna kalaman na ɓatanci, inda ta yi wa shafin na ta da cewa Musulunci, addini ne da bashi da zaman lafiya. Ba yan wallafa waɗan nan kalaman da jaridar ta yi, a ƙasa da sa'a guda sai da jami'an gwamnatin Faransa suka karance ta baki ɗaya. To amma duk da irin damuwar da ake nunawa kan zanen ɓatancin, babban editan jaridar ko a jikinsa.

epa02989335 Employes stand in front of the offices of French satirical magazine 'Charlie Hebdo', in Paris, France, 02 November 2011. The editorial offices of the satirical weekly were firebombed early on 02 November, the same day it put out an issue poking fun at the Islamic faith. Police were unable to confirm that the attack was linked to the issue, which went on sale well after the 2 am (0100 GMT) attack. However, the editor of Charlie Hebdo said he had received threats before the attack. EPA/MAXPPP/OLIVIER CORSAN EPA/MAXPPP/OLIVIER CORSAN FRANCE OUT --- BELGIUM OUT
Mai aikatan jaridar Charlie Hebdo a harabanr ofishintaHoto: picture-alliance/dpa

"Eh gaskiya ne abinda muka wallafa tsokala ce, amma ai tun shekaru 20 abinda muke yi kenan, sai dai a duk lokacin da ka sa wani abinda ya shafi addinin Islama, komi ƙanƙancinsa sai a yi ta ruruta labarin"

Wannan dai abune dake jawo taƙaddama, inda dama can jaridar Charlie Hebdo ta taɓa wallafa wasu kalaman ɓatanci. Amma ga mabiya addinin Islama wannan ba abun lamuncewa bane. Kamar yadda shugaban majalisar Musulmai ta ƙasar Faransa ke cewa, yanzu kam an kawo su iya yuwa.

"Mun kaɗu da irin wannan adawar da ake nuna addinin Islama. A yanzu haka irin martanin da ake mayarwa yana tayar mana hankali, tun bamu kai ko ina fil din ɓatanci da aka yi a Amirka, sai ga kuma wani rikicin ya bullo"

A French policeman stands guard outside the headquarters of the satirical weekly Charlie Hebdo in Paris, Wednesday, Sept. 19, 2012. Police took up positions outside the Paris offices of the satirical French weekly that published crude caricatures of the Prophet Muhammad on Wednesday that ridicule the film and the furor surrounding it. The provocative weekly, Charlie Hebdo, was firebombed last year after it released a special edition that portrayed the Prophet Muhammad as a "guest editor" and took aim at radical Islam. (Foto:MIchel Euler/AP/dapd)
Yan sanda a Paris ke gadin ofishin jaridar Charlie HebdoHoto: dapd

Wannan zanen ɓatancin dai ya zo ne a dai lokacin da ake ci gaba da yin bore a faɗin duniya bisa kalaman ɓatancin da wani Film a ƙasar Amirka ya yi, inda aka samu zubar da jini bisa boren da aka yi. Kuma koda a ƙasar Faransa an nuna adawa da wacan Film ɗin. Kamar sauran yan siyasa ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya fito a fili ya bayyana ra'ayinsa kan zanen ɓatanci da aka yi wa addinin Musulunci.

"A gaskiya akwai wayewa da zurfin tunani. Amma a wannan abunda ya ƙara zuba man fetur cikin wuta, ra'a yina a fili yake, ban amince da hakan ba. A ɗaya gefen bama so mu hanawa jama'a faɗin albarkacin bakinsu, amma kuma dole a nemi mafita kan yadda za a riƙa yin hakan ba tare da muzantawa wani ba"

Ga shi dai babban editan jaridar ta Charlie Hebdo wanda ta wallafa zanen ɓatancin, yana ganin kalaman firayim minista da na ministan harkokin wajen Faransa tamkar tunzara jama'a ne su yi bore.

To Amma ga malaman addinin Islama kamar su Imam Tareq Oubrou da ke limancin wani masallaci a ƙasar Faransa akwai shawara bisa yadda musulmai za su mayarda martani.

"Amsa mafi dacewa bisa irin wannan tsokala shine, ayi shiru, kada ma akula wanda yi"

Ita dai gwamnatin Faransa ta ɗau matakan riga kafi, kan zaton abinda zai iya biyo bayan zanen ɓatancin da jaridar ta wallafa, inda ta rufe ofisohin jakadancin ƙasar ta Faransa a ƙasashe dada na duniyar musamman inda musulmai suka fi rinjaye.

Mawallafa: Johannes Duchrow / Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu