Martanin Amurka ga ƙasar Iran
May 9, 2006Talla
Amurka ta yi shaguɓe ga wasikar da shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya aikewa shugaban Amurka George W Bush. Ahemedinejad yace wasiƙar ta baiyana shawarwari tare da matakan da zaá bi domin warware fargaba da kuma damuwar dake tsakanin ƙasashen biyu. Sai dai kuma a hannu guda Amurkan tace wasiƙar bata baiyana masalaha ba a game da taƙaddamar da ake ta nukiliyar Iran ɗin. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice tace wasiƙar wadda ke zama ta farko tsakanin shugabannin Iran da Amurka a tsawo shekaru 27 bata ce komai ba na sasanta muhimmin batun da ya fi ɗaukar hankalin duniya a tsakanin ƙasashen biyu.