1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin duniya bayan zaben Kirimiya

March 17, 2014

Kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta sha alwashin daukar matakai a kan Rasha, bayan da al'ummar yankin Kirimiya na kasar Ukraine suka zabi su koma karkashin ikon Rashan.

https://p.dw.com/p/1BQik
Hoto: Reuters

Ministocin harkokin kasashen ketare na Kungiyar ta EUi za su gana a wannan Litinin a birnin Brussels domin tabka muhawara a kan irin takunkumin karyar tattalin arzikin da za su kakaba wa Rasha, wadda suka hadar da hana 'yan kasar takardun izinin shigowa nahiyar Turai wato Visa da kuma rike kudadensu da ke ajiye a bankunan Turan.

A nasa bangaren shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce kuri'ar raba gardamar da al'ummar yankin na Kirimiya suka kada halartacciya ce, inda ya shaida wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merekel cewa an gudanar da zaben ne a karkashin dokokin kasa da kasa. Ya kuma ce zai mutunta bukatar al'ummar yankin na Kirimiya.

A nata bangaren Merkel ta bukaci da a fadada shirin tsaro na hadin guywa da nahiyar Turai a yankin na Kirimiya. Shi ma Firaministan riko na Ukraine Arseniy Yatsenyuk ya bukaci da a tura jami'an sanya idanu na kasa da kasa zuwa yankin.

Kaso uku bisa hudu na kuri'un raba gardamar da al'ummar yankin na Kirimiya suka kada na nuni da cewa sama da kaso 95 na al'ummar yankin sun amince su koma karkashin ikon kasar Rasha. A nan gaba kadan ake sa ran majalisar wakilan kasar Rashan za ta amince da dokar da za ta bawa yankin na Kirimiya da ya balle daga kasar Ukraine damar komawa karkashin ikon Rashan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Auwal Balarabe