1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin duniya kan harin kasar Pakistan

Yusuf BalaDecember 16, 2014

kasashen duniya sun yi tofin Allah tsine ga harin da Taliban ta Kai Peshawar, yayin da firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya ce za su ci gaba da yaki da 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/1E5pZ
Pakistan Taliban-Überfall auf Schule in Peshawar 16.12.2014
Hoto: Reuters/K. Parvez

Al'ummomin kasa da kasa sun yi tir da mummunan harin da kungiyar Taliban ta kai Peshawar na kasar Pakistan. Tuni dai kasashen duniya irinsu Amirka da Faransa da Birtaniya da ma Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana bakin cikinsu game da wannan ta'asa. Mutane akalla 130 ne suka hallaka a wannan hari, galibinsu kananan yara.

Tuni dai firaminista Nawaz Sharif ya bayyana cewa ba za su taba sassautawa ba a yaki da masu tada kayar baya. Ya ce "Ina ganin wannan yaki da fafutuka ba zamu saurara ba har sai mun ga bayan ta'addanci a wannan kasa"

Ita ma wannan yarinyar mai fafutukar ganin an bar yara sun je makaranta Malala Yusuffzai daga kasar ta Pakistan wacce ta samu lambar yabo ta zaman lafiya a duniya , ta bayyana kaduwa ta da jin wannan labari, wanda ta bayyana da cewa "Abu ne mai susa rai da aka kashe yaran cikin ayyukan ta'addanci a yankin na Peshawar. Yara cikin kayan makaranta basu taba ganin wani abu mafi muni ba kamar wannan abin Allah wadai".