Martanin duniya kan harin Spain
August 18, 2017Firaministar Britaniya Theresa May ta ce ya zama wajibi a hada karfi don yaki da ayyukan ta'addanci, don a gudu tare a tsira tare, a cewar ta duk kasashen duniya ne ke fuskantar wannan annoba ta barazanar ta'addanci. A na shi bangaren Firaminstan kasar Spain Mariano Rajoy ya jadadda bukatar tashin kasashen duniya tsaye don yakar ta'addanci.
Kasar Poland kuwa a ta bakin ministan harkokin cikin gidan kasar Mariusz Blaszczak ta ce duk da cewa Poland ba ta fuskantar barazanar mayakan IS, duk da haka akwai bukatar shugabannin kasashen Turai su matsa kaimi wajen dakile ayyukan ta'addanci a nahiyar.
Rahotanni daga kasar Spain na cewa akwai yiwuwar direban da ya kutsa motar cikin cunkoson jama'a na daga cikin mutane biyar da jami'an tsaron suka halaka a lokacin da suka yi kokarin shawo kan lamarin a ranar Alhamis.
Mamata da kuma wadanda suka sami rauni a harin sun kunshi 'yan kasashe 35 da suka kunshi Jamus da Faransa da Benezuwela da Australiya, da Ireland, sai Peru, da Aljeriya da kuma kasar Chaina.