1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Duniya kan rikicin gabas ta tsakiya

November 16, 2012

Tarayyar Turai da Amurka na goyon bayan Izraela dangane da ci gaba da gasa wa al'ummar zirin Gaza tsakuwa a hannu, akan abun da suka kira matakan kare kanta.

https://p.dw.com/p/16kk5
Hoto: Reuters

 A daidai lokacin da suke nuna nadama da fararen hular ɓangarorin biyu da rikicin ke ritsawa dasu, kasashen yammaci na turai sun jaddada bukatar 'yan Hamas su kawo ƙarshen hare-haren makaman rokoki da suke kaiwa yankin kudancin Izraela. Kwamishinar kula da harkokin ketare ta tarayyar turai Catherine Ashton wadda ta bayyana hakan, ta shawarci Izraela da ta tabbatar da cewar, martaninta bai shige na irin harin da Hamas ke kaiwa yankun Bani Yahudun ba.

Shima ministan harkokin wajen jamus Guido Westewelle ya ɗora alhakin kazantar halin da ake ciki dangane da rikicin yankin gabas ta tsakiya akan ƙungiyar Hamas....

 Yace " tsanantan wannan rikici ya ta'allaka ne da  harba rokoki da Hamas ke ci gaba dayi daga zirin Gaza, wanda ya raunata mutane da haddasa asarar abubuwa masu yawa a ɓangaren Izraela. Izraela nada 'yancin kare kanta, da al'ummata. Amma duk da haka ya zamanto wajibi a dauki matakan da suka dace na kare tsanantar wannan yanayi, tare da kare al'umma daga ci gaba da tagayyara".

Ägypten Kandil zu Besuch in Gaza mit Ziad al-Zaza
Majinyata daga hariHoto: Reuters

Shi kuwa mataimakin mai bawa gwamnatin Amurka shawara kan lamuran cikin Ben Rodes, kira yayi ga ƙasashen dake da ɗasawa da Hamas kamar Masar, Turkiyya da wasu ƙasashen Turai, da su yi kira ga ƙungiyar da ta dakatar da tsananta wannan rikici.

To sai dai a yayin da ƙasashen Yammaci na Turai da  ma amurka ke ganin da cewar cin zarafin Palastinawa da Izraela ke yi, Turkiyya na da ra'ayin cewar al'ummar Gaza na da 'yancin yin fafutuka domin kwatar wa kansu 'yanci. A martaninsa kan wannan rikici na yankin gabas ta tsakiya, priminista Recep Tayyip Erdogan yace, zan tattauna wannan batu da shugaba Barack Obama na Amurka a wannan juma'ar. Bugu da kari ganawarsu da shugaba Mohammed Morsi na Masar a ranar asabar zai yi nazarin batun.

Shi ma shugaba Abdullah Gul na Turkiyya, bayyana wannan cin zarafin da ƙasar ta Bani Yahudu kewa larabawan Palastinu da kasancewa zuba jarin jini domin zaɓe. Gul ya kwatanta wannan yanayi da ake ciki da shekaru huɗu da suka gabata, lokacin da Izraela ta kashe palastinawa 1,500 gabanin zaɓen ƙasar.

Tania Krämer wakiliyar DW ce data sha da ƙyar daga rikicin na zirin Gaza, wadda ta ce " na kasance a yankin na tsawon kwanaki biyu, sa'annan na samu nasarar ficewa, abunda yawancin Palastinawa basu da 'yancin yi. Hare hare ne na dindindin daga sararin samaniya, kana ga kuma wanda akeyi daga cikin Teku, zaka ji karar makamai daban daban, waɗanda baka ma san daga inda wannan tashin hankali yake ba, ballantana ka kare kanka"

Ägypten Kandil zu Besuch in Gaza
Priministan Masar Hisham Kandil a GazaHoto: Reuters

Wakilin Iraki a ƙungiyar ƙasashen larabawa yayi kira ga larabawan da suyi amfani da albarkatun Man da suke da shi a matsayin makamin tursasa wa Amurka da Izraela akan hare haren na Gaza. Qais al-Azzawy yana mai ra'ayin cewar  tattali a matsayin makami yana da tasiri  wajen kwato wa al'ummar Palastinu 'yancinsu.

Ɗaruruwan Palastinawa nedai suka gudanar da zanga-zangar yin Allah wadan hare haren na Izraela a sassa daban daban na ƙasar Lebanon.

Za'ayi sauraron sauti daga ƙasa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita           : Mohammad Nasir Awal