Martanin Hukumomin Sudan ga kalamomin Kofi Annan a game da Darfour
September 12, 2006Hukumomin Sudan, sun maida martani, ga kalamomin sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Kofi Annan, a game da yankin Darfur.
A jawabin da ya yi jiya, gaban komitin Sulhu Koffi Annan ya zargi hukumomin Khartum da yin watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta, da aka cimma a birnin Abuja, na taraya Nigeria, ta hanyar tura dubunan dakaru a yankin, wanda a halin yanzu, ke ciki gaba da ɓarin wuta, ga mazauna yanki.
Koffi Annan, ya bayyana damuwa, a game da halin da yankin darfur ke ciki, wanda har ma ya danganta da yanayin ƙasar Rwanda, a shekara ta 2004.
Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia,yayi kira ga hukomimin Sudan sun amince,, su karƙi dakarun shiga tsakani na ƙasa da ƙasa.
A fusace, Sudan ta maidawa Annan martani, tare da danganta shi ,da zama karen farautar Amurika.
Kazalika, ta jaddada matsayin ta, na ƙin amincewa da dakarun Majalisar Dinkin Dunia,a yankin Darfur.