1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin India da pakistan kan harin jirgin kasa daya kashe mutane 66

February 19, 2007
https://p.dw.com/p/BtwB
Jirgin zumunci da aka kaiwa harin bomb
Jirgin zumunci da aka kaiwa harin bombHoto: AP

Magabatan kasashen Pakistan dana India na cigaba da´yin Allah wadan harin boma bomai da aka kaiwa jirgin fasinja dake zirga zirga tsakanin kasashen biyu,wanda ya kashe kawo yanzu mutane 66 baya ga wasu adadi da suka jikkata da safiyar yau.

Prime minisatn India Manmohan Singh da monistocin harkokin cikin gida Shivraj Patil da na sufurin jiragen kasa Lalu Prasad,da shugabar majalisar dokoki Somia Gandhi,da sauran manyan jamian kasar India sun bayyana bakin cikinsu dangane da dumbin asaran rayuka da akayi a hadarin jirgin kasan.

Prime minisatan ya lashi takobin gurfanar da wadanda kweda alhakin wannan harin gaban kuliya,ayayinda Mr Prasad wanda ya ziyarci inda hadarin ya auku,ya dangana wannan harin da wadanda basa muradin a samu zaman lafiya da ake kokarin tabbatarwa tsakanin India da Pakistan.

Adangane da hakane ministan harkokin sufurin jiragen kasar ya tabbatar da gudanar da bincike kan wadanda keda alhakin,tare da biyan kudaden diyya wa wadanda suka rasa yanuwansu a wannan hari.

Dayake yin tofin Allah tsine akan wadanda suka kai wadannan hare hare na boma bomai akan wannan jirgin zumunci wanda ake kira Samjhauta Express,shugaba Parvez Musharraf na Pakistan ,yace bai zai taba yarda wasu masu munanan akidoji su kawo cikas cikin tattaunawar samar da zaman lafiya tsakanin kasashen India da Pakistan din ba.

Yace irin wannan mugun nufi bazai haifar da komai ba face dada inganta bukatar samarda da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.Akan hakane shugaba Musharraf ya jaddada bukatar shugabannin kasashen india da pakistan su dada zage dantse wajen ganin cewa haka ta cimma ruwa a wannan tattaunawa ta hadin gwiwa.

Itama mai magana da yawun ministan kula da harkokin ketare na Pakistan Tasnim Aslamcewa tayi….”Munyi Allah wadan wannan hari akan jirgin pasinjojin da kakkausar murya ,kuma muna mika taaziyyarmu zuwa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.Akasarin pasinjoji dake cikin wannan jirgi na zumunci,yan kasar Pakistan ne .Adangane da hakane gwamnati ke kokarin daukan nauyin iyalan wadanda hadarin ya ritsa dasu,domin su samu sukunin isa inda hadarin ya auku.

To sai dai sakamakon wannan hadarin na jirgin pasinja tsakanin kasashen India da Pakistan,an dauki tsauraran matakan tsaro abirnin New Delhi dake zama fadar gwamnatin India,da sauran sassa daban daban na wannan kasa,musamman tsakanin India da Lahore da bus bus dake bin wannan hanya.

Wasu tagwayen boma bomai nedai suka tarwatse acikin jirgin kasa na poasinja daya taso daga India zuwa pakistan,inda gobara ta biyo nan take wanda ya haddasa mutuwan mutane 66 nan take baya ga wasu adadi masu yawa da suka jikkata,harin da magabatan kasar suka bayyana da kokarin zagon tattaunawar sulhunta kasashen biyu makwabta dake adawa da juna na lokaci mai tsawo.