Martanin Iran a game da Ihsanin kungiyar tarayyar turai
June 21, 2006Talla
Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad yace suna nazarin tayin Ihsanin da kungiyar tarayyar turai ta gabatarwa kasar kuma zasu bada amsa a cikin watan Augusta da zarar sun kammala nazari. Da yake tsokaci, shugaban Amurka George W Bush yace watannin da Iran din ta dauka domin bada sun yi yawa, yana mai cewa ba abu ne da zai dauki kasar Iran din wani dogon lokaci ba kafin ta yi nazarin tayin wanda yake a fayyace. A Iran din shugaban kasar Mahmoud Ahmedinejad na fuskantar matsin lamba daga yan raáyin rikau ya yi fatali da tayin Ihsanin baki dayan sa. Ayatollah Ahmad Jannati ya baiyana tayin da cewa abu ne kawai da kasashen turan suka tsara domin biyan bukatun su.