Martanin Iran a kan makaman Nukiliyan Amurka
May 4, 2010Talla
Iran ta bayyana mallakar makaman Nukiliya 5,000 a ɓangaren Amurka, a matsayin rashin adalci da barazana ga zaman lafiya a Duniya baki ɗaya. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Tehran Ramin Mehmanparast ya ce akwai bukatar gudanar da bincike dangane da yawan makaman Nukiliyan Amurkan. A jiya ne dai a karon farko, Amurkan ta fito fili wajen sanar da cewar tana mallakar makaman Nukiliya kimanin 5,113. Kazalika kakain na Iran yayi watsi da zargin da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tayi wa Shugaba Ahmadinejad, na adawa da Amurka a taron Majalisar Ɗunkin Duniya na hana yaɗuwar makaman Nukiliya a birnin New York.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu