Rikicin Iran da Amirka
May 17, 2006Cikin wani jawabi da aka dauka kai tsaye a gidajen telebijin na kasar,shugaban kasar ta Iran Mahmud Ahmedinajad ,ya fadawa wani gangami na dubban jamaa a garin Arak cewa,kasashen yammacin duniya suna neman basu ihasani ne a madadin gwal ko albarkatu da suke da su,yace ba zasu amince su karbi wani ihsani da zai maye gurbin abinda suke da shi ba.
Yace kasar ta Islama ba zata mika wuya ga bukatun dakatar da aiyukanta na inganta sinadaren uraniyum ba,wanda ake tsoron zata kera makaman nukiliya da shi.
Yace su yanzu ba ihsani suke bukata ba, batun hakan ma bata taso ba,abinda suke bukata shine ayi adalci.
Shugaban na Iran ya kuma sake barazanar janyewar kasarsa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya tare da hana supetocin hukumar kula da yaduwar nukiliya ta kasa da kasa tashoshin nukiliyarsa.
Mahmud Ahmedinajad yace,sun amince tun farko da dakatar da aiyukan nukiliyan har na tsawon shekaru 2,wanda yace jamaar Iran basu ji dadinsa ba,saboda haka a cewarsa,Iraniyawa ba zasu taba bari su sake shiga irin abinda suka shiaga a baya ba,sakamakon dakatar da shirin a baya.
Inganta sinadaren na uraniyum yana taimaka samarda mai ga injunan nukiliya da zasu bada karfin hasken wutar lantarki,haka kuma zaa iya kara sarrafa shi ta yadda zaa iya kera makaman nukiliya,Iran dai tace inganta sinadaren domin samarda wutar lantarki ne kuma tana da yancin yin hakan karkashin yarjejeniyar ta hana yaduwar makaman nukiliya.
Yanzu haka dai manyan kasashen turai suna kokarin tsara wani ihsani ne da zai kunshi taimako ta fanning ciniki da fasahar zamani,wanda suke fata zai janyo hankalin Iran ta dakatar da shirinta na nukiliya.
Kakakin maaikatar harkokin wajen Burtaniya ya fadawa AFP cewa,tun farko an shirya cewa,komitin sulhu zai sake duba shi a ranar jumaa,amma yanzu an dage ganawar tasu sai nan da kawanaki 10,saboda baiwa kasashe 3 na kungiyar taraiyar turai damar sake shiraya game da shawarwarinsu.
Har yanzu dai akwai sabanin raayi tsakanin membobin komitin sulhun akan yadda zaa bullowa alamarin na Iran,idan tayi watsi da wannan tayi na bayan nan.
Amurka da kasashen turai 3 wato Burtaniya da Jamus da Faransa,suna son komitin sulhun ya bullo da wani kudiri wanda zai tilasatawa Iran a hukunce ta dakatar da inganta uraniyum,amma kasashen Sin da Rasha suna ganin cewa,hakan zai sake dagula alamarin ne,ya kuma bude hanyar daukar matakin soji akan kasar ta Iran.
A dai jawabin nasa na yau Ahmedinajad yace,kasashen yammacin duniya ba zasu samu nasara ba,saboda basa bisa kan gaskiya,kamar yadda kowa ya sani cewa ramin karya kurarre ne.
Shugaban na Iran ya kuma sake barazanar cewa,kasarsa zata bi turbar da Koriya ta arewa ta bi,muddin dai anci gaba da matsa mata lamba.
Yace,kasashen yammaci su daina daukar matakan da zasu sanya wasu kasashe da kunyoyoyi janyewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya,wanda zai janyo rushawar hukumar baki daya.