Martanin Iran game da zanga-zanga a Masar
February 7, 2011'Yan Iran ba su samun wasu labarai na kirki a game da halin da ake ciki na faɗi-tashi a duniyar Larabawa, kamar yadda Mohammed Sadegh Javadi Hesar ya nunar. Ɗan jaridar, kuma babban editan haramtacciyar jaridar nan mai suna Tous, yana ɗaya daga cikin mutane 'yan ƙalilan da har yanzu suke da ƙarfin zuciyar magana da kafofin yada labarai na ƙetare.
Ya ce: "Mahukunta a Iran suna da irin tasu fassarar game da abubuwan da ke gudana a Masar. Suna nunar da cewar zanga-zangar ta adawa ce da gwamnatina kama karya, kamar misali juyin juya halin da Iran ta yi kan tsohuwar gwmanatin Shah a shekara ta 1979. Mahukuntan suna kuma maimaita kiransu na cewar wai zanga-zangar ana yin ta ne fuskar addinin musulunci a ƙasar ta Masar.
Ranar Jumma'ar da ta wuce, a lokacin sallar Jumma'a, shugaban Musulmin Iran, Ayatollah Ali Khameini ya kwatanta zanga-zangar da ake yi a Masar da Tunisia a matsayin alamar da ke nunar da farkawa ta addinin musulunci. To amma washegari, ƙungiyar nan ta 'Yan uwa Musulmi ta mai da martani da cewar zanga-zangar ta Masar ba ta da wata danganataka da addinin musulunci, amma zanga-zanga ce ta adawa da gwamnatin mulkin kama karya da rashin daidaituwa, kuma zanga-zanga ce da ta haɗe dukkanin addinai da ɗarikoki a ƙasar.
A bisa duban farko, za'a ga kamar dai masu mulki a Iran suna nuna goyon baya su ne ga 'yan zanga-zanga a Masar, a matakansu na lumana na neman haƙƙinsu da ƙarin demukuraɗiya a ƙasar. Shugaban majalisar dokoki, Ali Larijani har ma ya baiyana suka ga matakin toshe kafofin Internet, wato yanar gizo. To amma idan aka yi la'akari da amfani da ƙarfi da mahukuntan na Iran suka yi wajen kwantar da zanga-zangar da ta biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa da kuma hana gabatar da rahotanni game da haka, ana iya cewa wannan matsayi na shugabannin na Iran kan halin da Masar take ciki bai wuce munafinci ba.
'Yan adawa a Iran yanzu suna ƙoƙarin amfani da halin da ake ciki domin cin ribarsu. Mir Hussein Mussawi da Mehdi Karrubi da ke wakiltar 'yan adawar sun nemi izinin hukuma su shirya zanga-zangar goyon bayan takwarorinsu na Masar da Tunisiya ranar 14 ga watan Fabrairu. Seraj Mirdamadi, ɗan jarida, kuma tsohon jami'in kampe na Mussawi, ya kwatanta wannan shiri na 'yan adawa a matsayin wata dabara ce mai ma'ana.
Ya ce: "Amsar da za mu samu a game da neman izinin shirya zanga-zangar ba ta da muhimmanci, saboda ko ta ina aka duba, mahukuntan dai suna ganin mutuncinsu zai zube. Idan har suka amince da wannan buƙata, dubban mutane za su hau kan tituna, abin da zai zama sabon ƙalubale ga gwamnati. Idan kuma suka ƙi amincewa da bukatunmu, wanda wataƙila hakan za su yi, za'a gane cewar shugabannin maƙaryata ne, abin da zai zama tilas su fito su yi wa jam'a bayanin dalilansu.
Seraj Mirdamadi da ke zaune a Paris yanzu, ya ce idan aka sami nasarar sanarwa jama'a, waɗanda yawancinsu talakawa ne da ke zaune cikin mummunan halin talauci game da muhimancin tashi tsaye su nemi haƙkinsu, hakan yana iya jan hankalin dubbansu su fito kan tituna su yi zanga-zangar adawa da gwamnatin ƙasar ta Iran.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Halima Balaraba Abbas
A ƙasa, za ku iya sauraron ƙarin rahoto akan Masar.