Martanin Iran game da ƙarin takunkumi
January 24, 2012Bayan da ƙungiyatr tarayyar Turai ta haramtawa Iran safarar man fetur zuwa ƙetare, a wani matakin hana ta ci gaba da shirin bunƙasa Nukiliyar ta, wani jigo a majalisar dokokin ƙasar ta Iran ya yi allah wadai da takunkumin da Turai ɗin ta amince da shi, yana mai kwatanta hakan da cewar a fakaice wani salo ne na yaƙi, inda kuma ya ƙarfafa barazanar da ƙasar ta yi a baya na toshe jigilar man fetur da manyan jiragen daƙon man fetur na ƙasashen duniya ke yi ta hanyar tekun Fasha.
Ko da shike ƙwararru a harkar soji na dasa ayar tambaya game da ko Iran tana da ƙarfin hana jigilar manyan jiragen ruwan, amma Amirka da ƙawayenta sun yi barazanar ɗaukar mataki - idan har ta yi hakan. Bayan sanya hannu akan takunkumin karya tattalin arziƙin da tarayyar Turai ta yiwa Iran, firaministan Birtaniya David Cameron, da shugaban Faransa Nikolas Sarkozy da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa, inda suka buƙaci Iran ta dakatar da shirin nukiliyar ta.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou