Martanin Jamus kan harin brinin Santambul
January 14, 2016Wannan hari dai da ya rutsa da 'yan kasar waje mafi yawansu Jamusawa na zuwa ne daidai lokacin da Turkiyya ke cigaba da fuskantar barazanar tsaro daga ciki da wajen kasar. Shugaba Racep Tayyib Erdogan dai ya ce maharin dan Siriya ne sai dai ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere zufin bincike ne kawai zai fayyace gaskiya.
Har wa yau, ministan cikin gidan na Jamus kore tunanin da ake da shi cewar Jamus aka nufa da wannan hari inda ya ke cewar ''bisa abinda muke da shi a yanzu, ba alamar cewa harin kan Jamusawa kawai aka shirya shi. Don haka ba shi da alaka ga shigarmu kawacen yaki da ta'addanci. Wannan harin a binciken da muke da shi yanzu an kitsa shi ne kan jama'a kawai".
Yanzu haka dai hukumomi na Turkiyya sun ce suna cigaba da gudanar da bincike kan wannan hari na ta'addanci inda ake cigaba da tsare mutane. Ministan cikin gidan Turkiyya Efkan Ala ya ce ''bisa abinda ya shafi harin Istabul an tsare mutane bakwai, bincike na ci gaba da gudana cikin kyakkyawan tsari''.
Jamus dai ta bakin ministan cikin gidanta Thomas de Maiziere dai ta ce harin ba zai kawo sabani tsakanin Berlin da Ankara ba kuma ba zai kai ga lalata alakar da suka kulla kan yakar ta'addanci ba musamman ma dai abin da ya danganci kungiyoyin da ke dauke da makamai kuma suke da'awar jihadi.