Martanin Jamus kan yarjejeniyar nukiliyar Iran
November 25, 2013Kasashen shida da suka jagoranci kulla yarjejeniyar sun hada da biyar masu kujerar dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, wato Amirka, da Faransa, da Birtaniya, da Rasha, da kuma China.
Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya jagoranci tawogar kasar yayin tattaunawar, kuma ya nuna farin ciki kan matsayar da aka cimma:
"Wannan yarjejeniya ce mai kyau, wadda za ta cimma wani abu. Muna da manufa kan dakile shirin makamin Iran, wannan abun muke neman kankarewa."
Mahukuntan kasar ta Jamus suna fata Iran za ta cike sharudan yarjejeniyar, saboda hake ne zai kare kasar daga duk wani takunkumi kan shirin nukiya nan da watanni shida masu zuwa.
Ruprecht Polenz tsohon dan majalisa daga jam'iyyar CDU mai mulki na zama masani kan harkokin da suka shafi kasar ta Iran, ya yi gargadi bisa bin sawun yarjejeniyar:
"Kasar Iran tana babban aikin nan da watanni shida masu zuwa, domin ta yi abin da ya dace, wanda aka amince da shi na dakile shirinta."
Ya kara da cewa sassauta takunkumi zai taimaka wa dangantaka ta kasuwanci da Jamus ke sha'awa da kasar ta Iran. Kuma ci gaba da ba da hadin kai daga bangaren Iran shi ne kawai abin da zai tabbatar da duk wata alaka ta gaba.
Anasa bangaren Omi Nouripur na jam'iyyar kare muhalli ta the Green, wanda kuma yake da sassala daga kasar ta Iran, ya ce wannan ya zama abin yabawa, saboda shekaru biyu da suka gabata, babu wanda zai yi tunanin haka zai kasance. Nouripur ya kara da cewa:
"Jamus tana taka mahimmiyar rawa ko wani lokaci da aiki da sauran kasashen duniya kan dakile shirin na nukiya. Wannan karon harda kasashen Rasha da China ba nahiyar Turai kadai ba, Amirka tana cikin gamayyar, wannan babban abu ne mai wahala. Wannan nasara ce."
Tuni Firamnistan Izira'ila Benjamin Netanyahu ya soki matakin inda ya kira yarjejeniya da kuskuren tarihi, wadda za ta taimaka wa Iran samun makamun nukiya.
Shugaban Amirka Barack Obama ya kira Netanyahu ta wayar tarho, domin ba shi tabbacin cewa Amirka tana kan matsayin kare muradun Izira'ila. Yarjejeniyar ta birnin Geneva ta amince sassauta takunkumi kan kasar ta Iran nan da watanni shida, yayin da kasar za ta dakile duk wani shirin bunkasa makamashin nukiyar.
Daruruwan mutane a Tehran babban birnin kasar ta Iran, sun yi tarba ta gwarzaye wa jami'an kasar da suka halarci taron tataunawar ta birnin Geneva da ke kasar Switzerland, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Mohammed Javad Zarif, wanda mutane suka rera masa wakolin jakadan zaman lafiya.
Yanzu haka farashin gangan danyen man fetur ya fadi kashi biyu cikin 100, bayan kulla yarjejeniyar, inda farashin ya koma dala 108.54.
Mawallafi: Suleiman babayo
Edita: Saleh Umar Saleh