EU ta damu ziyasar Ben-Gvir a Al-Aqsa
January 4, 2023Talla
Jakadan hulda da kasashen ketare na kungiyar Josep Borrell ne ya bayyana hakan a birnin Brussel na kasar Beljiyam, yana mai cewa a matsayinsu na Tarayyar Turai sun damu kan matakin na Ben-Gvir, wanda ya saba da abin da aka amince da shi.
A cewarsa dama tuni tashin hankali da asarar ayuka suka karu a yankin a makonnin baya-bayan nan. Ya kara da cewa kungiyar ta EU na kira ga duka bangarorin biyu, su yi kokarin yayyafawa matsalar ruwa ba wai ruruta wutar trikicin ba.
Tuni dai a nasu bangaren, Falasdinawan suka shiga tattaunawar gaggawa domin sanin matakin da ya kamata su dauka bayan ziyarar ta Ben-Gvir a Masalacin na Al-Aqsa.