Martanin kasashen duniya game da rahoto akan Iran
February 22, 2007A dai watan disamban bara ne komitin sukhu ya amince da wani kuduri na lakabawa Iran takunkunmi muddin dai bata cimma wannan waadi da aka diban mata ban a dakatar da shirin nata na nukiliya.
Rahoton dai ya bayaiyana cewa Iran taki amincewa ta bada hadin kanta game da wanan batu,inda take ci gaba da hakikancewa shirinta na zaman lafiya ne kuma domin anfaninta na cikin gida.
Shugaban Iran Mahmud Ahmedinajad ya kara sanartda da cewa Iran din zata dakatar da shirin nata muddin dai sauran kasashen yammacin duniya musamman Amurka suma sun dakatar da nasu shiri na nukiliya.
Ita dai gwamnatin Amurka dai ta baiyana rashin jin dadinta game da wannan rahoto.Kakakin fadar white house Gordon Johndroe yace wannan rahoto ya sanyaya gwiwar Amurka.
Sakatare janar na MDD Ban Ki Moon yace batun nukiliya na Iran yana da muhimmancin gasket ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma batun hana yaduwar makaman nukiliya a duniya,ya kuma yi kira ga Iran data bada hadin kanta ba tare da bata lokaci bat a kuma shiga tattaunawa da sauran kasashe domin kawo karshen rikicin cikin lumana.
Kasar Israila babbar abokiyar gaban Iran tace har yanzu akwai damar bin hanyar diplomasiya,mataimakin ministan tsaron Israila Ephraim Sneh yace har yanzu baa kure hanyar diplomasiya ba,akwai damar sake lakabwa Iran din takunkumi inji shi,wadanda zasu iya karya tattalin arzikin gwamnatin kasar.
Yace kasashen duniya suna da damar yin hakan kafin daukar wasu matakan nan gaba.
Ita kuwa gwamnatin Burtaniya cewa tayi har yanzu tana nan da tayin da akaiwa Iran din a watan yuni na bara cewa kasashen yammacin duniya zasu bata dukkanin abinda take bukata na game da samarda makamashin nukiliya irin na zamani.
Ministar harkokin wajen Burtaniyan Margaret Bekett tace tunda dai Iran taki karbar wannan tayin tare kuma da yin watsi da waadin da aka bata,babu abinda ya rage illa suyi kokarin daukar matakan komitin sukhu wanda za maida Iran saniyar ware cikin kasashen duniya.
Iran din dai a nata bangare tace tana nan akan bakanta na ci gaba da shirin nata.
Mataimakin shugaban hukumar makamashin atom na Iran Muhammad Saeedi yace wannan rahoto ya nuna cewa hanya kadai da zaa bi wajen magance wannan matsala itace a koma teburin tattaunawa da nufin cimma yarjejeniya da zata samu karbuwa ga dukkan bangarori da abin ya shafa.
Yace game da batun dakatar inganta maadinan uraniyum da rahoton yayi,saboda kuma yin hakan baya bisa dokar kasa da kasa,kuma baya bisa kaidojin yarjeniyoyi na kasa da kasa,saboda haka Iran ba zata taba amincewa da shi ba.