1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Pakistan kan zargi game da Osama

Joanna ImpeyMay 3, 2011

shugaban Pakistan Asif Ali Zardari ya ce Amirka ce ta hana ƙasarsa rawar gaban hantsi da za ta bata damar cafke Osama bin Laden shugaban Al-Qaida.

https://p.dw.com/p/117zR
Shugaba Asif Ali Zardari na Pakistan yayin tattaunawa da 'yan jaridaHoto: AP

Shugaba Asif Ali Zardari na Pakistan ya kare gwamnatinsa dangane da zarginta da ake yi da rashin taɓuka wani abin a zo a gani, domin kakkaɓo shugaban ƙungiyar Al-Qaida Osama Bin Laden daga maɓuyarsa da ke kusa da cibiyar horas da sojojin ƙasar. Cikin wata ƙasida da aka wallafa a wannan talata a jaridar Washington Post, shugaban ya ce ƙasar Amirka ce ta mayar da hukumomin ƙasar na tsaro ciki har da ta leƙen asiri saniyar ware. Sai dai Zardari bai bayyana dalilan da suka sa jami'an tsaron ƙasarsa kasa gano inda Osama Bin Laden ya fake ba duk da kusanci da gidan da ya ɓoye ke da shi da Islamabad babban birnin.

Shugaba Barack Obama ya nunar da cewa za a sami kyautatuwar al'amuran tsaro a duniya bayan kashe Osama Bin Laden da sojojin Amirka suka yi. Dama dai Bin Laden shi ne mutumin da Amirka ta fi nema ruwan a jallo tun bayan ƙaddamar da harin ta'addaci na birnin New-York shekaru kusan goma ke nan da suka gabata. Sai dai Sakatariyar Harkokin Wajen Amirka wato Hillary Clinton ta yi gargaɗi game da yiwuwar ɗaukar fansa daga ƙungiyoyin ta'addanci a sassa sassa daban daban na duniya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza sadissou Madobi