Iran: Mayar da martani kan takunkumin Amirka
November 8, 2018Anan Ali ne ke zaune a shagonsa na sayar da kayan kida irin na Piano a wannan karo ya samu lokaci yana dan taba kidan, yana siyar da wadanna kaya ne kawai, amma a wannan lokaci ba kasafai ake samun masu siyan kaya ba.
Anan an sakamu cikin tsaka mai wuya an sa takunkumi kan irin kayan da muke siya kamar daga kamfanin Yamaha a Japan, don haka ba mu da dama ta saya yayin da a bangare guda kuma su ma masu saya ba sa zuwa saboda tsadar kayayyakin.
Kamfanonin na kasa da kasa ba su da dama ta yin kasuwanci da Iran su kuma yi da Amirka, dalilin wannan takunkumi na mahukuntan birnin na Washington. Tun bayan da Shugaba Donald Trump na Amirka ya fice daga yarjejeniyar makamashin nukiliya da Iran a watan Mayu tattalin arzikin kasar sannu-sannu ke kasa, Mahukuntan na Tehran dai sun zargi Washington da kokari na hambarar gwamnati da irin wannan salo kamar yadda Shugaba Hassan Rouhani ya bayyana.
Shugaba Rouhani dai ya ce za su kauce wa takunkumin sai dai bai ba da bayanan dalla-dalla kan hanyoyi da za su bi ba, a kalla dai Amirka ta kyale Iran ta ci gaba da siyar da mai ga kasashe takwas ciki har da China amma Girka da Italiya da Turkiyya na samun kusan rabi na man da suke bukata daga Iran kan haka ne ma Fuat Oktay mataimakin shugaban Turkiyya ke caccakar matakin na Amirka.
Mutanen kasar ta Iran dai yanzu hankalunsu ya karkata kan kasashen Turai ta yadda za a samu hanyar ciniki da kamfanoni na kasar ta Iran kasancewar daga Turai kasashen sun fitar da wani tsari na musamman ko da yake an samu tsaiko daga bangaren na Tehran wacce ke da muradin ganin kasashen da suka cimma yarjejeniyar ta 2015 sun sake matsa kaimi wajen ganin sun rike yarjejeniyar wacce ita ma Amirkar kofa abude take gareta muddin ba ta zo da kaka gida ba a cewar Rouhani.