1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan Masar kan takarar Al-Sisi

Umaru AliyuJanuary 28, 2014

Al'ummar Masar na ci gaba da nuna goyon bayansu ga takarar Abdulfatah al-Sisi wanda bayan an yi mi shi ƙarin girma, ana sa ran zai ajiye aikin soji ya shiga siyasa

https://p.dw.com/p/1AyRV
Verteidigungsminister Abdel Fattah al-Sisi
Hoto: picture-alliance/dpa

Kiran da majalisar kolin Masar ta yi wa ministan tsaron kasar Abdulfattah Al -sisi da ya tsaya takarar shugaban kasa, bayan karin matsayi da tayi masa, daga janar zuwa filmashal ya jawo kace-nace tsakanin yan kasar.

Sa'dan Fawaz, tsohon ma'aikaci a cibiyar sanin makamakar mulki da dabarun kare kasa, ya bayyana dalilinsa na yin maraba da wannan mataki

"Sisi kwararrran soja ne, natsatsste, mai himma, gogaggagen dan siyasa, kasantuwarsa tsohon shugaban leken asirin soji, ya san ciki da waje na matsalolin kasa, uwa uba, gashi kuma dan baiwa mai kuma son addini."

Wani ma'aikacin gwamnati da ya yi ritaya shi ma cewa yake

"Sisi ne kadai zai iya ceton kasar nan ya tsamota daga mawuyacin halin tsaro da tattalin da take ciki, ga shi da kishin kasa, kai ni ina ganin a danka masa ragama ma, ba sai anyi wani tsabe ba."

Wata dattajiya ma cewa take

Ägypten Demonstration Plakat General Abdel Fattah al-Sisi
Hoto: REUTERS

"A gani na, shi ya dace da mulkin kasar nan a yanzu. Bayan shekaru na zaman kara zube da yamutsi, ba wanda zai iya daidaita kasar nan kan ba soja ba."

Wani matashi dan kungiyar Tammarud da ta jagoranci yin bore a Mursi kuwa cewa yake

"Ni kam bana son ya tsaya takara,domin zai fada cikin tarko ne,mutane suna da dogon buri,kadan basu gani a kasa ba,bashi kadai za,ayi wa bore ba,hard a su kansun sojoji."

Martanin 'yan adawa

Ita kuwa wannnan dalabar cewa take

"Sisi mutumin kirki dake da kishin kasa, amma hanyar da ya biyo don ya zama shugaban kasa, ban a raba daya biyu kan cewa,zaiyi mulki makamancinn mulkin Mubarak ne"

Shi kuwa wannan da aka kasha dan uwansa a zaman dirshan din Rab,atul adawiyya cewa yake

"Mutumin da ya kakkashe mutanan ne kana yak one sun ne za,a zaba shi shaugaban kasa?Mukan mun gama.Ba,abin d azan ce,sai Allah ya nuna mana ranar tozartarsu."

Shi kuwa Muhammad Jawadi, mashahurin mai fashin bakin siyasar kasar ta Masar cewa yake

"Daman a ce muku ba wanda yake yin juyin mulki don wani sai don kansa. Muddin sisi bai zama shugaban kasa ba,ya tabbatar cewa,duk sabon shugaban kasar da zai zo zai dinga dari dari dashi,domin ya san shi maci amana ne. Don haka, ko da zai karar da rabin yan kasar nan ne,zai yi mhakan don ya zama shugaban kasa."

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Pinaɗo Abdu Waba