1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan Najeriya a kan ziyarar Goodluck Jonathan a Chadi

Muhammad Al-Amin September 10, 2014

Jama'a sun yi tir da matakin shugaban Najeriya na zuwa Chadi tare da tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sherif wanda ake zargi da tallafa wa Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1DA3e
Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Abin tambaya a nan shi ne a matsayinsa na wa aka gayyace shi ya tafi wannan waje ? A matsayin gwamnan Borno ko kuma a matsayinsa na wa, tun da ai akwai gwamna mai ci na Borno wanda shi ne hahkkin mutane jihar suke wuyansa, me ya sa ba a tafi da shi ba sai wani ?

'Yan Najeriya na tambayar kansu dalilan tafiya ziyarar tare da Ali Modu Sheriff

Irin Tambayoyin ke'nan da‘yan Najeriya musamman ‘yan arewacin ƙasar ke yi tun bayan da ya bayyana cewar Shugaban Jonathan ya je ƙasar Chadi tare da ganawa da Shugaban Idriss Deby. A kan matsalolin tsaron Najeriya tare da tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sherif wanda ake zargi da tallafa wa Ƙungiyar Boko Haram. Yawancin jaridun Najeriya sun wallafa hotunan shugaba Jonathan da Shugaba Deby tare da Ali Modu Sheriff abin da ya bai wa yawancin al'ummar ƙasar mamaki. Ko yaya mutane jihar Borno suka ji da samun wannan labari.

Nigeria Abuja Militärparade
Hoto: DW/U. Musa

Ali Modu Sheriff ɗin dai har yanzu bai ce komai ba dangane da wannan ƙorafi

wani mazaunin garin Maidugri ya bayyana ra'ayinsa a kan wannan batu.

Nigeria Goodluck Ebele Jonathan Komitee zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz
Hoto: DW/U. Musa

''Waɗanda ba su amince ba da zargin da ake yi wa Ali Modu Sheriff ba,a yanzu sun dawo sun fara yarda da cewar lallai akwai hannunsa a cikin wannan rigingimu da mu ke fama da shi.''

Ya zuwa yanzu dai Gwamnatin jihar Borno ba ta ce komai kan wannan batu watakila saboda yanayin da ake ciki a wannan yankin da ake ganin yana neman maida hankali don taƙaita fargabar da al'umma ke ciki. Akwai kuma masu ganin lamarin bai zo da mamaki ba don sun san a rina musamman ganin yadda tsohon gwamnan tun bayan komawarsa jam'iyyar PDP yake samun wata kariya daga Gwamnati da ta kai ga buɗe filin jirgin saman Maiduguri inda ya sauka bayan a baya an rufe filin tare da hana wasu tashi daga filin saukar jiragen saman.