Martanin 'yan siyasan bisa zaɓen Bavariya
September 16, 2013A Tarayyar Jamus sakamakon zaɓen da ya gudana a yankin Bavariya, ya ɗauki hankali matuƙa a ƙasar, in da jam'iyyar CSU wanda dama can yaƙin tungarta ne ta samu gagarumar nasara, in da sakamakon zaɓen ya nuna ta samu rinjayen da take buƙata don kafa gwamnati ba tare da wata jam'iyyar ba. Ko da yake masu lura da siyasar Jamus, suna cewa dama can yankin Bavariya yanki ne na jam'iyar CSU mai ƙawance da jam'iyar shugabar gwamnati Angela Merkel. Amma dai ko ba komai sakamakon da ya ba su rinjaye, ya kuma kawo koma baya ga ɗaya daga cikin jam'iyyun dake gwamnati, wato jam'iyyar FDP wanda a shekara ta 2008, ta samu nasarar shiga gwamnatin hadaka a yankin na Bavariya.
Sakamakon zaɓen na jihar Bavariya dai an gudanar da shi ne mako guda gabanin zaɓen ƙasar baki ɗaya, inda kawo yanzu babu wanda ya son yadda za ta kaya bisa sakamakon zaɓen ƙasa baki ɗaya. A ɓangarenta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sakamakon na Bavariya wata alama ce ta nasara, to amma fa yankin Bavariya ɗaya ne daga sauran yankunan Tarayyar Jamus. Idan sauran zaɓuka suka tafi a haka to jam'iyar gawance a gwamnatin yanzu ta FDP, tabbas jami'anta sai su tattara kwamatsansu, amma shugaban jam'iyar na ƙasa Philip Rösler ya ce tamkar an tashe su daga barci ne.
"A Bavariya hannu agogo ya juya mana baya, amma a yanzu mun ɗaura damara ne ga zaɓen Tarayyar Jamus baki ɗaya, kuma wannan sakamakon tamkar wata fargarwace ga dukan 'yan jam'iyyarmu"
Wani abin da ya bayyana a zaɓen na jihar Bavariya shi ne, an samu ƙarin fitowar masu kaɗa ƙuri'a da kashi shida cikin ɗari, idan aka kwatanta da shekaru biyar na baya. Wannan kuwa dama abu ne da ya rataya kan jam'iyyu dake cikin gwamnati, domin yaƙin neman zaɓe ta hanyar jawo hankalin masu kaɗa ƙuri'a don fitowa, domin a baya an samu gagarumin koma baya ga Jamusawa masu fitowa don zaɓe, wannan fitowar kuwa babu wanda ta taimakawa kamar jam'iyar CSU, wanda hakan ya bata damar fitar da jam'iyar FDP. Wanda tun a shekara ta 2008 ake gwamnatin gawance da ita. Ga ɗaya daga jam'iyar da ta samu ɗan ci gaba a zaɓen, wato jam'iyar Social Demokrat, jagoranta ɗan takaranta na shugabancin gwamnatin Jamus wato Peer Steinbrück ya ce, kada fa magoya bayansa su saki jiki da wannan nasarar.
"Wannan sakamakon kada ya sa ku shiga girman kai, amma ku dubi ɗan ci gaba da aka samu ku yi alfahari da shi, wanda da shi za mu tinkarin zaɓen ƙasa a nan da kwanaki biyar, wannan tuni jam'iyyar mu ta shirya masa. Kuma da haka za mu kasance cikin shiri har ranar zaɓen gama gari".
In banda jam'iyar SPD, a sakamakon zaben na jiya dai, kusan dukkan ƙananan jam'iyyu sun samu koma baya, inda kuma ake ganin batun gwamnatin ƙawance da za a kafa babu wanda zai iya sanin yadda za ta kaya. Domin kuwa wani abu da zai zame wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel koma baya shi ne, akwai wasu gungun masu ƙyamar harkokin Tarayyar Turai da ake ƙiran yan AfD. A yanzu da ake batun ceto tattalin arzikin wasu ƙasashen EU, babu wanda ya son irin girman adawan da Merkel za ta fiskanta daga cikin jam'iyarta ta CDU, a ɓangaren masu adawa da harkokin EU. Sai dai sakataren jam'iyar CDU ta Angela Merkel na ƙasa wato Hermann Gröhe ya ce.
"Abu guda dai a fili yake, ko wace jam'iyya kanta ta ke tallatawa don samun amanna, don haka a ƙarara muke cewa, ko wane ra'ayi cikin ƙawancenmu, mai zaman kansa ne. Wato Jam'iyar FDP kanta ta ke yi wa yaƙin neman zaɓe, amma fa a abinda ke a zahiri, ko wace ƙuri'a ta biyu, ta Angela Merkel ce"
Yanzu haka dai jam'iyyu ko wace za ta farga baya ga wannan zaɓen na Bavariya, domin kuwa ɗan ci gaba da jam'iyar SPD ta samu, da kuma mummunan koma baya da jam'iyyar ƙawance a gwamnatin Merkel wato FDP ta samu, ya nuna cewa akwai jan aiki a dukkan ɓangarorin, domin samun nasarar kafa gwamnati, bayan zaben ƙasa baki ɗaya da zai gudana ranar Lahdi da ke tafe in Allah ya kaimu.
Mawallafa: Volker Wagener / Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu