1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Duwatsun kwalliya a Masar

Tilo Spanhel ZMA/LMJ
November 16, 2023

Tun zamanin Fir'auna ana hako duwatsu da sarrafa su a gefen Kogin Nilu na Masar, kuma tsawon shekaru da suka gabata an yi amfani da su domin gina Dalar Giza.

https://p.dw.com/p/4Ysd3
Masar | Fasa Duwatsu | Sana'a
Fasawa tare da sarrafa duwatsu domin yin kayan kawa, dadaddiyar sana'a ce a MasarHoto: Imago/imagebroker

A yanzu dai ana amfani da irin wadannan duwatsu ne, a dakunan girki na fadoji masu alfarma. Al-Kahira tana da tata gundumar mai suna Shaq El-Tho'ban, inda ake da shahararrun masu aikin sarrafa dutse. Shaq El-Tho'ban birni ne mai matsakaicin girma da ke cike da tarihi na tsawon shekaru, kan sana'ar tsararren dutse mai tsauri. Matasa ma ba a barsu a baya ba wajen aikin sarrafa duwatsun, sai dai wasunsu na yin aiki ba tare da kayan kariya kamar safar hannu ko tabarau ba. Dole ne kuma su yi aikin kamar yadda masu ciniki ke bukata, wato cikin sauri kana dutsen ya kasance daidai da girman da suke so. Mohamed Yassin mai shekaru 36 shi ne wata karamar cibiyar sarrafa duwatsun. Ga abin da yake cewa kan batun matakan kariyar: "A gaskiya, matakan kariya suna aiki a nan. Amma ma'aikatanmu ba sa son sawa. Suna tunanin zai kawo musu cikas cikin aiki."

Masar | Duwatsu | Kayan Kawa
A kan kawata masarautun Masar da irin wadannan duwatsuHoto: Prisma Archivo/picture alliance

Katanga ce kawai ta raba shagon Mohammed Yassin da takwarorinsa, kuma an kiyasin cewa akwai irin wadannan kananan shagunan aiki da masana'antu kusan dubu biyu da 500 a Shaq El-Tho'ban gundumar da ke wajen birnin Alkahira kuma suna jere a wuri guda. Titunan zuwa wadannan wuraren kanana ne, wadanda ke cike da ramuka masu zurfi da manyan injuna suka haddasa. Gundumar ita ce mafi mahimmancin wurin sarrafa marmara da sauran duwatsu a Masar kana daya daga cikin mafi girma, inda ake sarrafa duwatsun kawa a duniya. A cewar alkaluman hukuma masana'antar da ke Kogin Nilu, na daukar ma'aikata sama da dubu 200. Hakar duwatsu da sarrafa nau'ukan duwatsu dabam-dabam, na ba da muhimmiyar gudummawa ga tattalin arzikin Masar. Wannan ya faru ne saboda yawancin duwatsun da aka sarrafa ana fitar da su zuwa kasashen waje, kuma suna shigo da kudin da ake bukata cikin gaggawa.