Masar: Al Sisi zai yi mulki har zuwa 2030
April 16, 2019Talla
Gyaran dokar wanda za a gabatar da shi ga yan kasa don kada kuri’ar raba gardama na shan suka daga masu rajin kare dimukuradiyya wadanda suka baiyana cewa tamkar komawa ga mulkin kama karya ne shekaru takwas bayan juyin-juya hali da ya hambarar da mulkin shekaru 30 na Hosni Mubarak.
Yan majalisa 531 suka kada kuri’ar amincewa da daftarin yayin da yan majalisa 22 suka kada kuri’ar rashin amincewa dan majalisa daya kuma ya kaurace.
Kakakin Majalisar dokokin Ali Abdel Al yace wannan babbar rana ce ga kasar Masar.
Ana sa ran yan kasar za su kada kuri’ar raba gardama a farkon watan Mayu lokacin da musulmi za su fara azumin watan ramadan