1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: An daure masu kaifin kishin addini

Gazali Abdou Tasawa
September 24, 2018

Kotun kolin kasar Masar ta tabbatar a wannan Litinin da hukuncin daurin rai da rai kan wasu masu kaifin kishin Islama da ta samu da laifin kisan 'yan sanda.

https://p.dw.com/p/35PJ8
Ägypten | Massenverurteilungen mit 75 Todesurteilen für Anhänger der Muslimbruderschaft
Hoto: Reuters/A. A. Dalsh

Kotun kolin kasar Masar ta tabbatar a wannan Litinin da hukuncin daurin rai da rai kan wasu masu kaifin kishin Islama guda 20 wadanda a baya kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke wa irin wannan hukunci bayan samunsu da laifin kisan wasu 'yan sanda 13 a lokacin tarzomar da ta biyo bayan tsige tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi a shekara ta 2013 inda aka kashe mutane sama da 700. 

Kotun ta Allah ya isa ta ce mutanen ba su kuma da wata dama ta iya sake daukaka kara a nan gaba kasancewa wannan shi ne karo na biyu kuma na karshe da doka ta bai wa mutanen na iya shigar da kara a gabanta. 

Kazalika kotun ta daga ita sai Allah ya isa ta yanke hukuncin zaman akso na tsawon shekaru ashirin da biyar-biyar ga wasu mutanen 50, na shekaru sha biyar-biyar ga wasu mutanen 35 kana ta saki wasu kimanin 20.