Amnesty ta nemi sakin masu zanga-zanga
September 24, 2019Talla
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ta yi kira ga mahukuntan kasar ta Masar da su gaggauta sakin kimanin mutane 500 bayan da ta ce kundin tsarin mulki ya bai wa ‘yan kasa damar yin hakan cikin lumana.
Wannan na zuwa ne, bayan wani umarnin toshe kafofin sada zumunta na yanar gizo, wadanda masu fafutuka ke amfani dasu wajen gayyatar ‘yan kasar dasu shiga gangamin zanga-zangar da suke shirin gudanarwa a ranar Juma‘a mai zuwa, da suka yi wa take da ‘‘zanga-zangar ayi ta, ta kare‘‘ a wani yunkurin ganin bayan mulkin Shugaba Abdel-Fatah Al-sisi.