Boren kawo karshen gwamnati a Masar
September 24, 2019Zanga-zangar nuna kyama ga shugaban Masar Abdel-fattah al-Sissi ta barke a ko ina cikin fadin kasar da niyar kafa dan ba na ganin kawo karshen mulkinsa da masu boren ke yiwa kallo na dan kama karya bayan ya shafe shekaru kan madafan iko. Daruruwan masu zanga-zanga a manyan biranen Masar sun yi dandazo a dandalin Tahreer mai cike da tarihi da ke tsakiyar birnin Alkhahira da kuma sauran jihohin kasar, inda suka yi ta rera taken nuna kyama ga mulkin shugaban kasar.
Masu bore sun karba kira Wani matashin dan kwangila kuma mai shirya fina finai Muhammad Ali da ke gudun hijira a Spain ne ya yi kiran fitowa domin yin zanga-zangar, bisa zargin gwamnatin shugaban kasar al-Sissi da cewa ita ce mafi muni wajen barnata dukiyar kasa, bayan zubar da zubar da mutuncinta a idon duniya tare da shawartar 'yan Masar da su bazu kan titunan kasar don boren kawo karshen gwamnatin da ya kira azzaluma.
'Yan sanda na kallon masu zanga-zangaSai dai ba kamar yadda jami'an tsaron kasar suka saba nunawa ba, a wannan karo dai sojoji sun janye daga kan tituna, suma sauran jami'an kwantar da tarzoma sun takaita harbawa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa, lamarin da ya sanya da dama daga 'yan kasar na gasganta rashin jin dadin mulkin shugaba al-Sissi da wasu manyan hafsoshin sojan kasar ke nunawa, inda wasu ke zarginsa da cewa daga shi sai iyalansa ne kawai ke kwasar dukiyar kasar yadda suka ga dama.