1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin tsaro a tashoshin jirgin kasar Masar

Ahmed Salisu
May 13, 2018

Hukumomi a Masar sun tsaurara matakan tsaro a tashoshin jiragen kasa, kwana guda bayan zanga-zangar da jama'a suka gudanar don nuna rashin amincewarsu da karin kudin jirgi da aka yi wanda ya rubanya har sau uku.

https://p.dw.com/p/2xe16
Anschlag in Kairo 13.11.2014
Hoto: picture-alliance/dpa/Elfiqi

Jami'an tsaro suka ce baya ga matakan tsaro da aka kara, an kuma kame mutum 22 a tashoshi daban-daban na kasar ko dai daga bisani an saki da yawa daga cikin wanda aka kama din yayin da sauran da ke tsare da su ke ci gaba da amsa tambayoyi daga 'yan sanda. Hukumomi a kasar suka ce sun kara kudin jirgin ne don samun karin kudaden da za a fadada sufurin jirgin kasa a kasar sannan a samu sukunin kula da wanda ake da su yanzu haka.