Kwamitin sulhu ta yi taro a kan rikicin Gaza
May 16, 2021Wasu ayarin motoci sun yi jigilar tsallakawa da Falasdinawa 263 zuwa Rafa da ke yankin arewacin Sinai da yayi fama da rikici.
Kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Crescent da ke arewacin Sinai ta ce ta tura da tawagar likitocin bada agajin gaggawa don yin jigilar wadanda hare-haren baya-bayan nan ya rutsa da su. Rafah dai ta kasance hanya daya tilo zuwa ga wajen Gaza wadda bata karkashin ikon Isra'ila, inda Falasdinawa a kalla miliyan 2 ke zaune cikin talauci.
A yayin da yake jawabi a taron gaggawa na Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin ta bidiyo, ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya yi kira kan gaggauta tsagaita wuta, kana ya bukaci kwamittin sulhu da ya sauke nauyin da aka dora masa wajen sasanta rikicin.
A ranar Lahadin dai a kalla Falasdinawa 40 ne suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama, lamarin da ke zama mafi muni na asarar rayuka a rana guda.