1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitoci sun shiga yaki da kaciyar mata

Ramatu Garba Baba
February 6, 2019

Likitoci a kasar Masar, za su yi anfani da ranar bikin yaki da al'adar yi wa mata kaciya a duniya, domin wayar da kanun iyaye alfanun kauracewa dadaddiyar al'adar da ke haifar da tarin matsaloli na lafiya ga mata.

https://p.dw.com/p/3CnGm
Stephanie Sinclair - Gewinnerin des Anja Niedringhauspreis 2017
Hoto: IWMF/Stephanie Sinclair

Daruruwan likitoci ne, suka shirya gangamin na wannan Laraba, za su gudanar da aikin tare da lika wani dan kyale mai ruwan bula a jikin duk wata jaririya da aka haifa a wannan rana,  wanda alama ce da ke nuna kyamar wannan daddadiyar al'ada a fafutukar da ake na son ganin bayanta.

Masar na a sahun gaba a cikin kasashen duniya da ake da yawan mata da suke fama da illoli a sanadiyar kaciyar. A shekarar 2008 aka haramtata a yayin da a shekarar 2016 aka amince da dokar hukunta duk wanda aka kama da laifin yi wa ya mace kaciyar a Masar. Har yanzu ana ci gaba da gudanar da wannan al'ada.