Masar na zaben raba gardama
April 20, 2019Talla
A kasar Masar, ana ci gaba da zaben raba gardama bayan gyaran fuska da majalisa ta yi wa kundin mulkin kasar, da ka iya bai wa shugaban kasa damar zarcewa zuwa shekara ta 2030.
Tashar talabijin ta kasar ta nuno Shugaba al-Sisi lokacin da yake kada kuri'arsa da misalain karfe tara na safiya, da ma na wasu misrawan asassa daban-daban.
Sama da mutum miliya 61 aka yi wa rajistar zabe a Masar din wanda zai dau kwanaki uku.
Haka nan ma sauye-sauyen za su bai wa shugaban kasar damar nada manya a bangaren shari'a da kuma taka gagarumar rawa a kan al'amuran sojin Masar.
Zaben na zuwa ne yayin da wutar juyin juya hali ke ci a wasu yankunan larabawa da ke nahiyar Afirka, da masu da'awar jaddada dimukuradiyya ke turje wa masu mulki na mahadi ka ture.