1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: Shugaba Al-Sissi ya lashe zabe

Salissou Boukari
April 2, 2018

Hukumar zaben kasar Masar ta sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar da ya gudana na ranekun 26, 27,da 28 ga watan Maris da ya gabata, inda ba tare da mamaki ba, Shugaba Abdel Fattah al-Sissi ya lashe.

https://p.dw.com/p/2vNj3
Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sissi Hoto: Reuters

 Shugaba Al-Sissi dai ya lashe zaben ne da kashi 97,08 cikin 100 na kuri'un da aka kada, a gaban daya-dayan abokin takararsa Mussa Mostafa Mussa, da ake yi wa kallo a matsayin wani mai goyon bayan Shugaba Al-Sissin.

A zaben da ya gudana na wa'adin farko na mulkin na shi a shekara ta 2014,  Abdel Fattah Al-Sissi ya lashe zaben ne da kashi 96,09 cikin 100, inda a cikin shekaru hudu na mulki ya fatattaki masu adawa da shi na jam'iyyar 'yan uwa Musulmi, da ma masu ra'ayin sassauci na kasar ta hanyar daure duk wasu da ake ganin masu adawa da shi ne.

Shugaban mai shekaru 63 da haihuwa ya dauri a niyar wani sabon wa'adin mulki na shekaru hudu nan gaba. Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta sanar cewa ta matsu ta ga ta ci gaba da hular  da Shugaban na Masar bayan sake zabensa da 'yan kasar suka yi.