1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta ayyana dokar ta-baci

April 10, 2017

Hare-hare kan majami'u sun sanya gwamnatin Masar kafa dokar ta-baci a kasar a kokarin shawo kan rigimar tsaro da ke tayar da hankali a kasar.

https://p.dw.com/p/2axzH
Ägypten nach Anschlag auf Kirche inTanta
Hoto: Reuters/M. Abd el Ghany

Shugaba Abdel Fattah Al Sisi na kasar Masar, ya ayyana dokar ta-baci na watanni uku a kasar, bayan hare-haren boma-bomai kan wasu majami'u biyu na kasar a jiya Lahadi. Shugaban na Masar ya sanar da dokar ta-bacin ne cikin jawabin da ya yi bayan ganawa da majalisar tsaro.

Hare-haren da kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da su a biranen Tanta da kuma Alexandria, sun haddasa asarar akalla rayuka 44 na mabiya addinin Kirista da ke ibada a majami'un. Dokar dai yanzu ta kara wa jami'an tsaron kasar karfin gudanar da bincike da kuma kame ba tare la'akari da 'yancin zirga-zirga yadda aka saba ba.

Dama dai wani bangaren da kungiyar ke da karfi cikinsa a kasar, na karkashin wannan dokar. Kasar ta Masar dai ta sha fuskantar makamancin wannan matakin na tsawon shekaru, sai dai tsohon shugaba Mohamed Morsi ya cire shi cikin shekarar 2012.