Masar ta ce ba ta fara dasawa da Iran ba
September 2, 2012Gwamnatin Masar ta yi watsi da kalaman da Iran ke yi na cewar za ta gyara dangantaka tsakaninta da ƙasar Iran. Kakakin shugaban na Masar Yasir Ali ya ce ko kusa shugaba Mursi ba furta cewar zai maido da dangantaka tsakanin ƙasarsa da Iran ba. Mr. Ali Mursi ya ce ganawar da shugaba Mursi da Ahmediijad su ka yi lokacin taron 'yan ba ruwanmu da aka yi a Tehran, bai ta taɓo maido da danganta tsakanin kasashen biyu ba ko kuma batun sake buɗe ofishin jakadanci ƙasashen.
A ranar Alhamis din da ta gabata ce dai mukaddashin ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollah ya shaidawa kafar watsa labaran Iran ta Al-Alam cewar shugaba Mursi da Shugaba Ahmedinijad sun tattauna dangane da halin da ake ciki a Siriya da ma dai dangatakar da ke akwai tsakanin ƙasashen biyu wadda ta jima da lalacewa. Zuwan shugaba Mursi Tehran dai shi ne karo na farko da wani shugaban Masar ya yi ƙasar ta Iran tun bayan da dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu bayan juyin juya halin shekara ta 1979 da aka yi.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal