Masar ta ce Hamas kungiyar ta'addanci ne
January 31, 2015Talla
Hukumomin Masar na zargin wannan kungiya da ke rike da mulki a Zirin Gaza na Falasdinu da taimakawa masu tsattsauran ra'ayin addini kai hare-hare a kan jami'an tsaro a yankin Sinai. Ko da a wannan asabar sai dai hukumomin na Masar suka tabbatar da mutuwar wani jami'in ma'aikatar cikin gida a Sinai, inda 'yan bindiga suka kutsa gidanshi tare da harbeshi har lahira.
Tun dai bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Mursi ne hare-hare a kan 'yan sanda da kuma sojoji suka zama ruwan dare a yankin na Sinai sakamakon alwashin daukar fansa da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta sha alwashin yi. Magoya bayan Kungiyar 1500 aka kashe yayni da aka daure 15 000 daga cikinsu tun bayan da aka habarar da gwamnatin Mohamed Mursi.