An saki ma'aikacin Al-Jazira dayaa Masar
February 1, 2015Rahotannin sun tabbatar da cewa tuni Greste ya bar birnin Alkahira na kasar ta Masar zuwa Ostareliya da ke zaman kasarsa ta asali bayan da ya kwashe tsahon kwanaki 400 a gidan kaso
Ma'aikatan gidan talabijin na Al Jazeera uku ne da suka hadar da Peter Greste da Mohamed Fahmy da ke da shaidar zama dan kasar Kanada da kuma Masar sai Baher Mohamed dan kasar ta Masar suke tsare a gidan kaso a Masar sakamakon samunsu da laifin yada labaran karya da kuma goyon bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da gwamnatin kasar ta haramta, wanda kotun kasar ta ce ta yi kana ta yanke musu hukuncin shekaru 10 a gidan kaso.
Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar a saki Mohamed Fahmy nan da 'yan kwanaki, sai dai babu karin bayani dangane da makomar Baher Mohamed da ke zama dan asalin kasar ta Masar.