1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta tsaurara matakai kan iyakokinta

June 11, 2023

Masar ta sanar da daukar matakai masu tsauri a kan iyakokinta da nufin dakile kwararar 'yan gudun hijirar Sudan da ke tururruwa domin shiga kasar a kakarinsu na kaucewa ricikicin da ake yau da kusan watanni biyu.

https://p.dw.com/p/4SRJ4
'Yan gudun hijirar Sudan a iyakar kasar da Masar
'Yan gudun hijirar Sudan a iyakar kasar da MasarHoto: -/AFP via Getty Images

A sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Masar ta fitar ta ce kasar ta yi hakan ne domin daidaita al'amuranta na cikin gida a game shige da fice, da kuma takawa masu buga bizar bogi ta shiga kasar birki. Sanarwar ta kuma kara da cewa matakin ba yana nufin Masar ta rufe kofofinta ba ko kuma tana yunkurin kayyade adadin 'yan Sudan da take ba wa mafaka ba.

Tun kafin sanar da wannan mataki, kafafen yada labaran kasar Sudan sun ruwaito cewa a 'yan kwanaki biyun nan hukumomin na Masar sun bayar da umurnin hana 'yan gudun hijirar Sudan shiga kasar ba tare da mallakar tarkar izini ta biza ba.

A kalla dai 'yan gudun hijiran Sudan sama da dubu 200 ne suka tsere Masar tun bayan barkewar rikici a tsakanin manyan Habsoshin sojan Sudan a ranar 15 ga watan Aprilun da ya gabata baya ga dama da akwai wadansu 'yan Sudan din miliyan biyar dake zaune a kasar tun kafin fara yakin.