1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta tsawaita dokar tabaci

Yusuf Bala Nayaya
July 4, 2017

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi dai ya sanya dokar tabaci bayan kai hari kan wasu majami'u biyu na wasu mabiya darikar Coptic harin da 'yan ta'adar IS suka yi ikirari na kai shi.

https://p.dw.com/p/2fvo4
Ägypten al Sisi in koptischer Kirche in Kairo 7. Januar 2015
Hoto: Ahmed Gamel/AFP/Getty Images

Majalisar dokokin Masar ta amince da bukatar kara wa'adi na dokar tabaci a dukkanin fadin kasar da karin watanni uku kamar yadda shugaban Masar ya gabatar da wannan bukata.

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi dai ya sanya dokar tabaci bayan kai hari kan wasu majami'u biyu na wasu mabiya darikar Coptic harin da 'yan ta'adar IS suka yi ikirari na kai shi.

A cewar kamfanin dillancin labaran MENA ya jiyo kakakin majalisar dokokin kasar ta Masar Ali Abdel Aal a wannan rana ta Talata ya ce kara wa'adin dokar tabacin na dole ne duba da tabarbarewar tsaro, kuma karin dokar zai fara aiki ne adaga ranar goma ga watan Yuli.

Tun dai daga watan Disamba hare-hare kan 'yan darikar ta Coptic ya yi sanadi na rayukan mutane 100 banda wadanda suka samu raunuka.