Masar ta tsawaita wa'adin al-Sisi
April 17, 2019Talla
Majalisar mai wakilai 596 wadanda galibi ke goyon bayan Shugaba al-Sisi, ta amince da gagarumin rinjaye ne cikin watan Fabrairu kafin ta tabbatar da gyaran a ranar Talata.
Sai dai za a kada kuri'ar ra'ayin 'yan kasa a farkon watan Ramadanan bana, da ke iya kamawa a ranar biyar ga watan gobe na Mayu.
Idan kuma aka kammala kuri'ar ta raba gardama, shugabannin kasa a Masar za su rika yin shekaru shida ne sau biyu.
Hakan kuwa na nufin za a yi wa shugaba mai Abdel Fattah El-Sissi wanda ke wa'adinsa na biyu, karin wasu shekaru biyu na mulkin da yake kai.
Kazalika, zai sake takara a shekara ta 2024.