SiyasaSudan
Masar za ta dauki nauyin taron sasanta rikicin Sudan
May 29, 2024Talla
Babban burin taron da za a yi cikin watan gobe, shi ne samun yarjejeniyar samar da dawwamammen zaman lafiya da zai kawo karshen rikicin da Sudan ta fada a ciki.
Tun cikin watan Afrilun bara ne dai kasar ta Sudan ta fada yakin basasa, sakamakon takaddamar siyasa tsakanin sojojin kasar karkashen Shugaba Abdul Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo.
Dubban fararen hula ne dai aka yi kiyasin sun salwanta kawo i yanzu a kasar.
Muhimman kasashe Irin su Amurka da Masar da ma Saudiyya, sun yi ta kokarin samar da masalaha kan rikicin na Sudan amma lamarin ya ci tura.