1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar za ta fara raba wa talakawa kudade

August 29, 2024

Firaminista Mostafa Madbouly ne ya sanar da haka a Alhamis din nan, yana mai cewa hukumomin kasar sun yi ittifakin cewa raba wa mutane kudade zai fi alfanu kan biyan tallafi kan kayayyakin abinci da kasar ke yi.

https://p.dw.com/p/4k4aS
Hoto: Beata Zawrzel/ZUMA Press Wire/picture alliance

Firaministan ya ce yana sa ran matakin ya fara aiki a shekara mai zuwa matikar wasu bangarori na gwamnati suka amince da tsarin.

A halin da ake ciki, mahukuntan kasar Masar na biyan tallafi kan taliya da burodi ga mutanen kasar da ba su da karfin tattalin arziki, inda mutane miliyan 60 ke amfana ta hanyar sayen kayan masarufin a wasu shaguna na musamman da hukumomin kasar suka bude domin saukaka wa 'yan kasar radadin tsadar rayuwa.