Masar za ta sa ido kan masu shiga Intanet
September 2, 2018Tun a watan Yuli ne dai 'yan majalisa a Masar suka amince da kudirin dokar da za ta ba wa hukumar koli da ke lura da harkokin kafafen yada kabarai dama ta rika lura da abin da al'umma ke yi a shafukan intanet, musamman mutanen da ke da masu bin shafukansu da suka kai 5,000 a shafukan sada zumunta ko Blog ko kuma shafukansu na Intanet.
Wannan dai zai ba da dama ga wadanda aka ba wa alhakin lura da shafukan, su rufe ko dakatar da duk wani shafi da ya watsa labaran karya ko labarin da ka iya tada hankulan al'umma da haddasa rikici ko gaba tsakanin al'umma, ko kuma bata wa mahukunta rai.
Sai dai 'yan fafutika na kallon wannan doka a matsayin tarnaki ga mataki da ya yi saura a hannun al'umma da suke amfani da shi wajen bayyana abin da bai masu daidai ba a game da gwamnatin al-Sisi. Tuni ma dai tun kafin dokar ta fara aiki aka rufe wasu shafukan intanet kimanin 500.