An zabi Masar domin shirya AFCON ta 2019
January 8, 2019Talla
Shugaban hukumar ta CAF Ahmad Ahmad ne ya sanar da hakan a wannan Talata a karshen kuri'ar da kwamitin zartarwa na hukumar ta CAF ya shirya tsakanin kasar ta Masar da Afirka ta Kudu a wannan Talata a birnin Dakar na Senegal.
Kasashen na Masar da Afirka ta Kudu sun kawo daukin daukar nauyin gasar ta 2019 ne bayan da hukumar ta karbe daga hannun kasar Kamaru a bisa jinkiri wajen kammala gina filayen wasanni da wuraren karbar baki da kuma matsalar tsaro da kasar ke fama da ita a sakamakon hare-haren Boko Haram da kuma rikicin 'yan awaren yankin da ke magana da Turancin Ingilishi.
Za a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafar ta Afirka daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yulin wannan shekara ta 2019.