1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masarautar Bahrein ta rusa jam'iyar 'yan Shi'a.

April 15, 2011

Ma'aikatar shari'ar daular Bahrein ta rusa jam'iyar Al wefaq bisa umurnin sarki. Jam'iyar ta 'yan Shia' ta yi watannin biyu ta na bore da nufin tilasta wa sarki ƙaddamar da sauye-sauyen siyasa.

https://p.dw.com/p/10trY
Postar shugabannin jam'iyar 'yan Shi'a na BahreinHoto: dpa

Masarautar Bahrein ta ba da umurnin rusa jam'iyar 'yan shi'an ƙasar bisa zargin gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati ba tare da wani ƙwaƙwaran dalili ba. Ministan shari'ar ƙasar ya ce tuni ma'aikatarsa ta fara ɗaukan matakan aiwatar da umurnin daular, saboda barazana da jam'iyar Al Wefaq ke yi ga zaman lafiya.

Wannan yunƙurin dai na daga cikin tsauararan matakai da sarki Baherin wanda ɗan sunni ne ke ɗauka, domin kare gadonsa na mulki tun bayan da 'yan shi'a suka fara neman a aiwatar da sauye sauye a fiskar siyasa.Mutane aƙalla 30 ne dai suka rasa rayukansu tunbayan fara zanga-zangar ƙin jinin gwamnati watanni biyu ke nan da suka gabata.

Mawallafi:Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman